Kashi na 45 – Gidan Tarihi | Radio D Teil 2 | DW | 18.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 45 – Gidan Tarihi

A karshen zaman Paula da Philipp a Jena, sun ziyarci wani gidan ajiye kayan tarihi. A can ne suka ga masu hikimar da suka yi yayi a karni na 18.

Shi gidan tarihi na Jena ya fi karkata ne ga tarihin juyin adabin gargajiya. A nan masu ziyara kan ji bayani game da hikimomin wannan karni da kuma sauyin da aka samu a fagen wakoki. Wakilan Radio D sun raka masu saurare zuwa gidan tarihin, inda suka nuna musu hotunan masu hikima kamar su Fichte, da Novalis, da kuma dakin karbar bakin Caroline Schlegel.
Ganin yadda abubuwan ke ta faruwa a lokaci guda, ya sa Farfesa ya yi bayanin kalmomin mahadi kamar su "als" da "wenn", wadanda ake amfani da su wajen nuna faruwar abubuwa a lokaci guda.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa