Kashi na 44 – Garin masu hikima | Radio D Teil 2 | DW | 18.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 44 – Garin masu hikima

A karni na 18 garin Jena ya jawo masu hikima da yawa daga sauran garuruwa. Cikinsu akwai shahararren marubucin nan Friedrich Schiller. Philipp da Paula sun gabatar da wani wasan kwaikwayo a kan laccar da ya yi a Jena.

A wannan kashin masu saurare za su san labarin Schiller da Goethe ta hanyar komawa cikin tarihin Jena daga karni na 18. A nan ne Schiller ya yi laccarsa ta farko a lokacin yana da shekara 29. Fiye da dalibai 500 ne suka halarta. A sakamakon yawan masu sauraren laccar, sai da aka sauya wurin gabatar da ita.
Farfesa ya dawo da tunanin masu saurare daga karnin baya zuwa na yanzu, inda ya yi bayani a kan kalmar aikatau ta "werden" wadda ke nuni da lokaci na gaba.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa