Kashi na 43 – Shiri na musamman | Radio D Teil 2 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 43 – Shiri na musamman

Yanzu an kusan shawo kan matsalar hasken fitilar nan. Sai dai kuma Paula da Philipp ba su ji dadi ba, domin kuwa ga labarin nan duk ya fito a cikin jarida. Ko a ina abokan hamayyarsu suka samo labarin?

Paula da Philipp sun ga mummunan labari: akwai cikakken labarin wannan filtila mai mugun haske a cikin wata jarida. Wato, saura su bincike dalilin da ya sa ba a tsaron kofar kamfanin sosai. Sai 'yan jaridar suka nufi wurin. Suna fatan in sun kai za su ga ana hira da 'yan jaridu, ko kuma kakakin kamfanin yana bayani.
To, wane ne ya yi hira ke nan? Wannan rudanin ya sa shi ma Farfesa ya yi irin wannan tambaya, sannan kuma ya yi bayani a kan jawabi kai-tsaye da kuma a kaikaice.

Kwafa