Kashi na 42 – Aiki ya samu Eulalia | Radio D Teil 2 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 42 – Aiki ya samu Eulalia

Paula da Philipp sun kusa gano wannan al'amari. Yanzu haka dai sun san daga inda mugun hasken nan yake fitowa. Sai dai kuma Eulalia ba ta dawo daga leken asirin da ta tafi ba. Me ya faru?

Bayan Paula da Philipp sun gano daga inda hasken yake fitowa, sun sanar da kamfanin fitilun don a warware matsalar. Amma sun fi damuwa da bacewar Eulalia. Sai kawai 'yan jaridun suka ji wani kuka. Ko wani abu ya samu Eulalia ne?
Bayan wannan rintsi da aka shiga, yanzu masu saurare za su dan shakata da nazarin kalmomin nahawu. Farfesan yana bayani a kan wakilan suna na mallaka na mutum na uku, wato "sein" da "ihr".

Kwafa