Kashi na 39 – Ta′addancin fitila mai mugun haske a garin Jena | Radio D Teil 2 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 39 – Ta'addancin fitila mai mugun haske a garin Jena

Da isarsu garin Jena, sai Paula da Philipp suka shiga binciken wannan lamari na ta'addancin. Kafin haka ma ashe an sake aikata wannan lamari. To, me yake faruwa haka?

A kan hanyarsu ta zuwa otel, 'yan jaridar sun sami damar tambayar direban tasin da suke ciki a kan wannan abin da yake faruwa a gari. Sai ma kuma kawai suka yi kacibus da abin a gabansu: wani yana fasa maduban motocin mutane da fitila mai mugun haske. Ko wannan harin yana da nasaba da taron da aka yi ne yanzu haka a kan fitila mai haske a garin Jena?
Yanayin kalmomin nahawu dai a wannan darasi ba su da wahala. Farfesa ya yi bayanin kalmomin wuri da bayanau kamar su "mit", da "zu", da kuma "in" wadanda suke daukar jakada.

Kwafa