Kashi na 37 – Wasikun masu saurare | Radio D Teil 2 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 37 – Wasikun masu saurare

Yanzu Farfesa zai amsa tambayoyin masu saurare kan darussan da suka gabata. Zai yi amfani da faifan don nuna masu saurare cewa za su iya fahimtar abubuwa da yawa ba tare da sun fahimci kowace kalma da aka furta ba.

Wasikun masu saurare sun fi mayar da hankali ne a kan dabarun fahimtar maganar baki. Kamar koyaushe dai, Farfesan ya amsa tambayoyin masu saurare, tare da bayar da shawarwari a kan dabarun saurare da fahimta da kuma sanin kalmomi.
Daga cikin abubuwan da ya gabatar akwai yadda ake sanarwa cikin amsa-kuwwa, da yadda ake kira da amsa waya, da kuma yadda ake sanarwa ta rediyo. Haka kuma masu saurare na iya gane abubuwan da ake fada ta yadda ake sauya murya, da kuma ta kalmomin da aka sani, da kuma irin hayaniyar da ake ji a bayan fage. Haka kuma suna iya cankar ma'anar kalmomin da ba su sani ba daga yanayin da ake maganar.

Kwafa