Kashi na 35 – Beethoven na kida irin na Beethoven | Radio D Teil 2 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 35 – Beethoven na kida irin na Beethoven

Yan jaridar nan na Radio D har yanzu suna ta tunani ko zargin da daliban nan da ke hira ke yi ya zama gaskiya. Sai dai kuma mujiya Eulalia ta shiga gabansu, domin kuwa ta bankado wani abu a yawon da ta tafi cikin dare.

Mujiya Eulalia dai ta bayyana ne kwatsam a birnin Bonn, inda ta kawo wa Paula da Philipp agaji kamar yadda ta saba. Domin kuwa ta gano wane ne mutum wanda ke kada fiyanon nan. Haka kuma ta gano daga inda sautin kidan ke fitowa. 'Yan jaridar shirin Radio D din dai sun bi shawarar mujiya Eulalia, wajen yin hira da "Matashin Beethoven". To amma kuma a ina za su gan shi?
To, ko da Paula da Philpp har yanzu ba su yi nasarar gano dalilin da ya sa ake kade-kade cikin daren nan ba, shi kuwa Farfesa zai yi mana bayani ne a kan yadda za a gane sassan jumla.

Kwafa