Kashi na 34 – Fatalwa a gidan Beethoven | Radio D Teil 2 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 34 – Fatalwa a gidan Beethoven

Philipp da Paula na son gano mutumin da ke kada fiyano da daddare a gidan da aka haifi Beethoven. Sun dada samo muhimmin labari a wani gidan shan kofi da ke garin. Bakin zaren suka gano ko kuwa jita-jita ce?

Bayan Paula da Philipp sun zauna na wani dan takaitaccen lokaci a wani gidan shan kofi cikin gari, sai suka jiyo wata hirar da ta ja hankalinsu. Wasu daliban kade-kade ne su uku suke tattaunawa a kan mutumin da suke zargin shi ne ke kada fiyanon nan cikin dare. Paula da Philipp sun jiyo labarin wani dalibi gwanin kade-kade wanda kowa ke wa lakabi da "Beethoven".
A yayin da Philipp da Paula ke bibiyar ko wane ne mutumin da ke kada fiyano a gidan Beethoven, shi kuma Farfesa na can ya mayar da hankalinsa a kan bayanin tambayoyin da akan yi ba na kai-tsaye ba, wadanda ba sa dauke da kalamomin tambaya.

Kwafa