Kashi na 33 – Sabon abokin aiki | Radio D Teil 2 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 33 – Sabon abokin aiki

Jan ya fara aiki a Radio D a matsayin ma'aikaci. Amma Paula da Philipp ba su saurare shi ba saboda kwamfutar ofishinsu ta ba su da wani aiki. Wajibi ne 'yan jaridar su garzaya zuwa Bonn.

Yayin da Jan yake kokarin gane abokan aikinsa a ofishin Radio D, tuni an fara binciken rahoton farko. Ya zama dole Paula da Philipp su garzaya birnin Bonn. Domin kuwa a gidan da aka haifi Beethoven, wato shahararren marubucin nan na kade-kaden gargajiyar Turawa, wani abin mamaki na faruwa cikin dare. Don haka kowanne daga cikin 'yan jaridar ya kuduri aniyar binciko wannan labari.
Sai dai kuma, ba kamar abin mamakin da ke faruwa a gidan da aka haifi Bethoven ba, yau Farfesa yana bayani ne a kan tsarin kalmomin da ke cikin tambayoyin da akan yi ba na kai-tsaye ba.

Kwafa