Kashi na 32 – Tsakanin zomo da bushiya | Radio D Teil 2 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 32 – Tsakanin zomo da bushiya

Masu hikima dai kan ce "Kafarka ta kai ka" Sai dai kuma wani lokaci abin ba haka yake ba. Domin kuwa mujiya Eulalia ta kawo wa masu saurare wani labari a kan wata gasar tsere mai ban mamaki.

Lokacin labari ya yi a Radio D: Kamar dai irin gasar da take wakana a kauyen Grünheide, irinta ta taba faruwa a tsakanin namijin bushiya inda ya kalubalanci zomo da yake da dogayen kafafuwa, da su zo su yi tsere. Bushiya da matarsa suna so su koya wa zomo wani darasi.
Wannan labari dai an kawo shi ne a cikin sigogin kalmomin nuna aikin da aka yi a baya. Wannan dama ce da Farfesa ya samu domin yin bayani a kan kalmomin aikatau masu nuna aikin da aka yi a baya. Har ma kuma da fandararrun kalmomin aikatau da kuma irin yadda suke da sabani.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa