Kashi na 31 – Kowa ya shirya! | Radio D Teil 2 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 31 – Kowa ya shirya!

A kauyen Grünheide abubuwan mamaki ne suke ta faruwa. Ta yaya ma za a ce mota kirar Trabbi ta kai gaci kafin motar nan mai gudu Porsche? Sai dai kuma Paula fa ta hadu da Jan wanda ya san sirrin wannan al'amari.

A gaishe da Jan Becker, domin kuwa a tafiyarsu da Paula zuwa kauyen Möllensee, ta gano muhimman abubuwa. Lallai akwai wani coge a wannan gasa ta motoci. Don haka sai Paula ta fara bin diddigin dabarun da direban motar nan kirar Trabant ke amfani da su. To, ko me Philipp ya sani game da wannan gasa? Domin kuwa ya fada tarkon Günther, direban motar nan Trabant.
Amma wadannan dabaru ba za su yaudari Farfesa ba. A wannan darasi na nahawu ya yi bayani a kan sigogin kalmomi masu nuna aiki a baya. Haka kuma ba shi da wata matsala da fandararrun kalmomin aikatau kamar su "sein" da kuma "haben".

Kwafa