Kashi na 30 – Jan Becker | Radio D Teil 2 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 30 – Jan Becker

Can sai wani mutum ya kunno kai ta mashayar wanda Paula ta dauka zuwa Möllensee, inda nan ne karshen gasar. Me wannan bako ya sani game da gasar motocin mai ban mamaki, kuma me ce ce dangantakarsa da shirin Radio D?

Bayan da motar Philipp ta ki tashi, sai Jan Becker wanda suka hadu da Paula ba da jimawa ba a cikin mashaya ya kawo musu dauki. A yayin da Philipp ya tsaya a kauyen Grünheide, ita kuma Paula sai ta bi Jan a motarsa zuwa kauyen Möllensee. A nan ne ake sa gasar za ta kammala. A yayin da Paula take tafiya tare da wannan bako, ta fahimci abubuwa da dama da ya kamata a ce tuni ta san da su...
Shi ma kuma Farfesa ya yi waiwaye, inda ya duba kalmomin aikatau masu nuna yanayi kamar su “müssen” da “wollen” da kuma yadda ake amfani da su wajen nuna aikin da aka yi a baya.

Kwafa