Kashi na 29 – A cikin mashayar kauyen Grünheide | Radio D Teil 2 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 29 – A cikin mashayar kauyen Grünheide

Paula da Philipp sun fara yi wa mutane tambayoyi a cikin mashayar Grünheide. Duk mutanen sun gamsu motar nan kirar Trabbi ce za ta doke Porsche a gasar. Sai ba haka Philipp yake gani ba.

Paula da Philipp sun je wannan mashaya ce ta kauyen Grünheide don su binciko labari game da wannan gasa. Suna son su samu wani muhimmin labari daga teburin masu zuwa mashaya koyaushe. Bayan da Philipp ya dan shakata, sai kuma ya nemi mutanen kauyen da su zo a yi caca.
Farfesanmu dai yana ci gaba da mayar da hankali a kan siffofin nan na nahawu da ke kwatanta fifikon abu, musamman ta yadda siffofin wasulan kan sauya wajen nuna fifiko dabam-dabam.

Kwafa