Kashi na 28 – Gasa tsakanin mota kirar Trabbi da Porsche | Radio D Teil 2 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 28 – Gasa tsakanin mota kirar Trabbi da Porsche

Wani sabon aikin Paula da Philipp ya kai su ga wani karamin kauye a yankin Brandenburg, inda za a yi gasar tseren motoci ta musamman. Ga alama ba za bar 'yan jaridar Radio D a baya ba.

Wannan gasa dai ita ce ta jawo Paula da Philipp zuwa kauyen. Da farko kamar ba wani abu da yake gudana. Amma da isarsu kauyen Grünheide da ke yankin Brandenburg, sai abin ya fa burge su. Mutane sai dafifi suke a mashayar kauyen. Wani direban wata mota kirar Trabant sai kuri yake yana cewa motarsa ta fi mota kirar Porsche gudu.
Shi kuwa Farfesa wannan gasar motoci dama ta ba shi da zai yi nazarin kalmomin da ke nuna kamanceceniya. Wace mota ce ta fi gudu, kuma wacce ta fi mugun gudu a tsakanin motocin.

Kwafa