Kashi na 26 – Ban-kwana da Ayhan | Radio D Teil 1 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 26 – Ban-kwana da Ayhan

Wannan rana ce ta bakin ciki a ofishin Radio D. Domin kuwa Ayhan yana ban-kwana kuma zai koma kasar Turkiyya. Duk da cewa abokan aikinsa sun shirya masa walima ta ba-zata, wannan bai kwantar masa da hankali ba.

Paula ta zo aiki da safe ta samu kowa yana shirye-shiryen zuwa walima. Yanayin bai gamsar da ita ba: Ayhan fa barin Radio D zai yi ya koma kasar Turkiyya don ya taimaka wa babansa. Don yi masa ban-kwana, abokan aikinsa sun shirya yin wani takaitaccen jawabi da kuma wata kyauta domin su tuna masa da abokiyarsa mujiya Eulalia.
Don girmamawa ga wannan walima ta ban-kwana, shi ma Farfesa ya ajiye kundinsa na nahawu a gefe. Amma duk da haka ya yi cuku-cuku ya shigo da wadansu 'yan bayanai game da hardaddun sunaye.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa