Kashi na 23 – Kayar kifin ″shark″ | Radio D Teil 1 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 23 – Kayar kifin "shark"

Paula da Philipp sun warware matsalar ganin kifin "shark", sannan kuma sun sake gano wata damfara. Amma, har yanzu ba a gano dalilin da ya kawo wannan ba.

Yayin da ake neman mai wasan sululun kan ruwa, Paula da Philipp kuma sun hadu da wani mai iyo, sun kuma gano bakin zaren. Mai iyon nan ya razana yawancin mutanen birnin Hamburg saboda ganin kayar kifin "shark" din da ke bayansa. Amma me ya sa? A daya bangaren kuma, Eulalia ta bayyana a birnin Hamburg din don taimakawa. Ita ma ta gano wani abu.
Eulalia ta samo wata makama wadda ta yiwu, za ta taimaka wa Paula da Philipp -- wata dama ta yin alfani da shudadden lokaci. A kula da yadda aka hada kalmar da take nuna lokacin aikin da aka yi a baya.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa