Kashi na 21 – Kifin ″shark″ a Hamburg | Radio D Teil 1 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 21 – Kifin "shark" a Hamburg

Yayin da yanayin cikin ofishin Radio D ya zama mara dadi, Paula da Philipp sai suka ji dadin aikin da zai kai su bakin teku, inda aka ga wani kifin "shark" a gaba.

Paula da Philipp da Ayhan ba su ji ta dadi ba. Zafin cikin ofis din ya tsananta, ga shi kuma ko fanka ba su da ita. Paula tana so ma ta samu dama ta je bakin teku, sai kuma kwamfuta Compu ta bayar da wannan damar. Ya kamata 'yan jaridar su tafi Hamburg saboda an ce an ga wani kifin "shark" a bakin teku. Saboda cunkoson mutanen da suka je don su ga wannan kifi, Paula da Philipp ba su samu isa wajen ba.
Haka ma abubuwa suka dagule wa Farfesa, wanda yake ta kokarin shawo kan yadda zai gabatar da yadda kwayar kalmar jinsin namiji take karewa. Kalmar musantawa ta "kein" ma ta wannan hanyar take karewa.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa