Kashi na 20 – Ra′ayoyin masu saurare | Radio D Teil 1 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 20 – Ra'ayoyin masu saurare

Paula da Philipp na son jin ra'ayoyin masu saurare. Batun da za a tattauna a kai shi ne, "Shin karya laifi ce?". Masu saurare na iya bayyana ra'ayoyinsu kan wannan da'irar ta jabu, da halayyar manoman.

Tambayar da Paula da Philipp suka yi wa masu saurare ita ce, "Shin yin karya laifi ne?". Wannan tambaya ta samo asali ne daga irin abubuwan da suka faru a gonar nan ta hatsi, inda 'yan jaridar suka dauko rahotonsu. Shin ko abin da wadannan manoma suke aikatawa daidai ne? Ko kuma laifin 'yan yawon bude ido ne da suka zamo marasa wayo? Masu saurare dai ba su yi wata tambaya ba wajen bayyana ra'ayoyinsu.
Sai dai kuma akasin yadda 'yan jaridar suka yi tambayarsu ga masu saurare mai amsar "e" ko "a'a", shi Farfesa ya gabatar da wani darasi a kan jinsi a harshen Jamusanci. Ya nuna cewa kalmomin sunaye a Jamusanci na iya daukar jinsin namiji, da mace, da kuma na hadaka. An yi bayanin wadannan abubuwa a cikin wannan kashi ta amfani da kalmomin "der", da "die", da "das".

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa