Kashi na 19 – An kusa kaiwa gaci | Radio D Teil 1 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 19 – An kusa kaiwa gaci

Duk da cewa manoma ne suka yi wannan da'irar, har yanzu Eulalia ta yarda akwai aljanun samaniya. Binciken Philipp da Paula suke yi na damfarar nan ya kai su mashaya, suka yi hira da mazauna kauyen.

Paula da Philipp sun warware wannan siddabaru na da'irar amfani, amma har yanzu ba su tabbatar da cewa ko akwai aljanun samaniya ba ko babu. Me ake nufin da aljanun samaniya ne? Eulalia dai ta dage a kan ta taba ganinsu. Daga karshe dai sai 'yan jaridar suka tambayi wadansu baki a wata mashaya da ke wani kauye a kan abin da suka fahimta game da wannan da'irar.
Ziyara zuwa wannan mashaya wata dama ce ta gabatar da aikin a shudadden lokaci, musamman ta amfani da fandararriyar kalmar aikatau "sein". Haka kuma an sake bayanin kalmar aikatau mai nuna yanayi ta "können" a wannan kashin. A kula da yadda wasalin ya canja yayin hada kalmar da take nuna aikin.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa