Kashi na 17 – Amfanin gona mai da′ira | Radio D Teil 1 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 17 – Amfanin gona mai da'ira

Yayin da aka gano wata da'ira a gonar, sai Paula da Philipp suka shiga bincike. Shin aljanun samaniya ne suka sauka a wajen ko wani ne yake wasa da hankalin mutane?

Yayin da Ayhan ya isa ofishin Radio D, Paula da Philipp sun yiwo waje. An gano wadansu irin da'irori a gonar hatsi, kuma ba wanda ya san wanda ya yi su. Ba 'yan jaridar ne kawai suke son ganin wannan abin mamaki ba, har 'yan yawon bude ido sun taru a wajen.
Wannan hayaniyar ta hada mutane dabam-dabam a wajen. 'Yan yawon bude ido suna so su gane wa idonsu, su kuma 'yan jarida suna so su warware matsala, su kuma manoma suna so su sami kudi. A lura da yadda ake amfani da kalmomin aikatau masu nuna yanayi a wannan kashin.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa