Kashi na 16 – Labarin Icarus | Radio D Teil 1 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 16 – Labarin Icarus

Labarin jarumin nan na tarihin Girkawa, wato Icarus, ya burge 'yan jaridar. Amma ko masu saurare sun san wane ne Icarus? Ga Paula da Philipp nan za su ba ku labarinsa.

A yayin da Paula da Philipp suka ga wani yaro ya yi shiga irin ta jarumin nan na Girkiwa, Icarus, sai wata dabara ta fado musu: ya kamata su gabatar da tarihin Girkawa a daya daga cikin shirye-shiryensu na rediyo. Labarin dai na wani matashi ne da ya ki daukar shawarar babansa mai suna Dädalus, har ta kai ga ya fado a lokacin da yake kokarin tashi sama. Shi bukatarsa kawai ya kai ga inda rana take, amma da ya tashi ya nufi kusa da ita, sai dankon da ke jikin fikafikinsa ya narke. Mahaifinsa ya fada masa cewa "Kar ka tashi can sama, kar kuma ka yi kasa-kasa." A wannan kashi an nuna yadda ake iya amfani da kalmar aikatau da ke nuna umarni don bayar da umarni ko neman wani abu. Da Icarus ya saurari gargadin da mahaifinsa ya yi masa, watakila da bai fado kasa ba.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa