Kashi na 13 – Litinin din shagulgula | Radio D Teil 1 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 13 – Litinin din shagulgula

Ba kowa ne yake murna da wannan bikin ba a Radio D. Aikin da aka ba wa Compus shi ne ya kai wadannan 'yan jaridar dajin nan mai suna "Black Forest", inda nan ne bikin ya fi armashi.

A wadansu bangarori na Jamus, ana yin bikin gargajiya ne cike da nishadi. A Radio D kuwa, wannan biki ya jawo hatsaniya. Paula ba ta ga dalilin zumudin da Phillip yake yi ba, saboda shigar da ya yi ba ta burge ta ba.
Abin da ya faranta wa Philipp rai shi ne, bincikensu ya kai su wannan dajin, inda mutane cikin shigar mayu ke sace motoci ana tsaka da shagalin bikin. 'Yan jaridar sun so su gudanar da wani shiri na kai tsaye, amma abin bai yiwu ba. A nan mayu suka jawo Philipp daga mota suka kuma sace shi.
Tsarin kalmomi a Jamusanci bai kai jidalin bikin nan ba. Wannan kashin ya mayar da hankali ne a kan bigiren aikau da aikatau.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa