Kashi na 10 – Ganawa da Sarki Ludwig | Radio D Teil 1 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 10 – Ganawa da Sarki Ludwig

Philipp ya sami wanda ya fito a Sarki Ludwig a wasan kwaikwayon, ya nemi su yi hira. Nan take sai ya gano muryarsa. Can kuma, wani bako ya bulla ofishin Radio D.

A can fadar Neuschwantein, Philipp gano wannan bakuwar fuskar ba tare ma da taimakon Paula ba: ashe wannan jarumin ne cikin wasan kwaikwayon da aka yi na Sarki Ludwig. Phillip ya yi amfani da wannan damar ya yi hira da mutumin. Yayin da ya dawo ofishin Radio D a Berlin, sai ya yi mamakin samun wata mujiya mai magana.
Wannan kashin cike yake da abin mamaki ga Philipp. Za ku ji yana ta cewa "Das glaube ich nicht" (wato: ban yarda ba) da kuma "Das weiß ich nicht" (wato: ban sani ba). Wannan wata dama ce ta ku kula da kalmar musantawa ta "nicht".

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa