Kashi na 09 – Kidan Ludwig | Radio D Teil 1 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 09 – Kidan Ludwig

Philipp ma ya gano wane ne wannan bakuwar fuskar. Ya ga wani talla a jarida a kan shagalin kade-kaden Sarki Ludwig. A hanyarsa ta zuwa can, ya yi hira da 'yan yawon bude ido da suka zo daga ko' ina cikin duniya.

Yayin da Paula ke zaune a ofis dinta a Berlin, Philipp kuma na can na sintiri a Munich. Bai san komai game da abin da Paula ta gano ba, sai dai shi ma a kan hanya yake. Wani talla a jarida a kan shagalin kade-kaden Sarki Ludwig ya ja hankalinsa. Kuma da ya hau bas, ya gana da 'yan yawon bude ido a kan tunaninsu game da shagalin bikin.
Ku yi ta yin bitar fahimtarku ta saurare a wannan kashin. A cikin bas din, za ku ji ana magana da harsuna dabam-dabam. Ku yi kokarin gano kalmomin Jamusanci. Za a gabatar muku da kalmar musantawa ta "nichts" da kuma inda take fitowa a bayan kalmar aikatau.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa