Kashi na 07 – Ludwig Sarki na tatsuniya | Radio D Teil 1 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 07 – Ludwig Sarki na tatsuniya

Paula da Philip sun gabatar da Sarki Ludwig ga masu saurarensu ta rediyo. Yanayin shigowar dare, da hayaniyar shagulgula da wadansu sababbin kirkire-kirkire, su ne abubuwan da suke nuni da yanayin Ludwig da zamaninsa.

'Yan jaridar sun ja hankalin masu saurarensu zuwa karni na 19. Sai suka hasko Sarki Ludwig mai son nishadi, da irin soyayyar da yake yi wa yanayi mai bishiyoyi da furanni, da kuma son da yake yi wa wakokin Richard Wagner, da dangantakarsa da 'yar'uwansa, Sarauniya Sissi. Kowa ya yi mamakin wani teburi da Ludwig ya kirkiro da kansa.
Wannan kashin yana magana ne a kan abubuwan da Sarki Ludwig ya fi so, wanda ya yi nuni ga koyon kalmar da take nuna "lieben" (so). Haka ma abin yake ga wannan kalmar ta "kommen" (zo), ita ma za ku ji ta.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa