Kashi na 06 – Ta yaya Sarki Ludwig ya mutu? | Radio D Teil 1 | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 06 – Ta yaya Sarki Ludwig ya mutu?

A can fadar Neuschwanstein, Paula da Philipp sun hadu da wata bakuwar fuska sanye da alkyabbar Sarki Ludwig. Sai suka yi wani dan bincike game da sanadin mutuwar Sarki Ludwig.

Wannan mutumin da ke sanye da alkyabbar Sarki Ludwig ta alfarma, na son su Paula da Philipp su dauka cewa shi ne ainihin sarkin. Ta yaya Ludwig ya mutu? Sai 'yan jaridar suka shirya wani wasa na rediyo don su haska wa masu saurare zargin mutuwar da Sarki Ludwig ya yi a tafkin Starnberg. Ba wanda zai iya tabbatarwa cewa kashe shi aka yi ko kuma shi ya kashe kansa.
Wannan ganawa da suka yi da wannan shu'umin mutumin wata dama ce ta jin bambance-bambance wajen magana tsakanin 'yan gida da kuma baki. Ku saurari yadda ake fadar taken ban-girma na "Sie" da na wanda ka saba da shi na "du." Lura da tushen kalmar aikatau "sein".

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa