Kashi na 02 – Waya daga Radio D | Radio D Teil 1 | DW | 16.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 02 – Waya daga Radio D

Philipp har yanzu bai samu hutun da yake so ba. Bayan gama fafatawa da kwaron da ya dame shi, sai ya fuskanci hayaniyar makwabta. Yayin da kwatsam aka yi masa waya daga Berlin, sai ya baro kauyen a gaggauce.

Bayan fafatawar da Philipp ya yi da kwari a can, sai ga karar zarto, da hayaniyar wani da yake koyon busa. Duk abubuwa dai sun taru sun dame shi. Don haka, yayin da Paula ta Radio D ta kira shi daga Berlin, sai Philipp ya sami dalilin katse ziyararsa ta kauye. Philipp dai ya yi ban-kwana da mahaifiyarsa wadda ba ta ji dadin tafiyarsa ba, daga nan sai ya garzaya babban birnin kasar Jamus.
Idan ma Jamusancinku bai nuna ba, za ku iya fahimtar abin da yake faruwa a wannan kashin. Kalmomin da ake amfani da su na yau da kullum, da kuma karin muryar da ake amfani da shi, za su taimaka muku wajen fahimtar shirin da kuma iya saurarensa.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa