Kashi na 01 – Ziyara zuwa kauye | Radio D Teil 1 | DW | 16.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 1

Kashi na 01 – Ziyara zuwa kauye

Philipp wani matashi ne, ga shi can yana tuka mota zai ziyarci mahaifiyarsa mai suna Hanne a kauye. Ya yi shirin shakatawa a can, amma kuma sai ya tarar da yanayin zaman kauye na da irin nasa matsalolin.

"Kauye da dadi yake!" in ji Philipp, a yayin da ya isa kauyen da mahaifiyarsa take, inda kuma yake son ya huta daga hayaniyar birni. Sai dai ba shanu da maguna kawai ya tarar ba, har ma da wasu halittun. Yana cikin shan kofi a lambu, sai wani kwaro ya bata masa lissafi. Daga nan sai abubuwa suka fara dagule wa Philipp.
Ko masu sauraro ba su iya Jamusanci sosai ba a yanzu, za su iya fahimtar abin da ke kunshe a wannan kashin. Don kuwa hayaniyar da ake ji a bayan fage, ta isa ta bayyana inda Philipp yake. A wannan kashin, za ku koyi yadda ake yin gaisuwa da ban-kwana.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa