1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta gargadi Jamus kan Huawei

Gazali Abdou Tasawa
November 27, 2019

Amirka ta yi kashedi ga kasar Jamus a game da duk wani shiri na damawa da kamfanin Huawei na kasar Chaina a aikin inganta harakokin sadarwar wayar salula a kasar.

https://p.dw.com/p/3TndS
Deutschland Mobilfunkausbau l Huawei 5G
Hoto: Getty Images/AFP/P. de Melo Moreira

A wata fira da babban mai bayar da shawara ga shugaba Trump kan harakokin tsaro, Robert O'Brien ya yi da jaridar der "Bild" ta nan Jamus, ya ce bai ji dadin yadda ma kasa mai da'awar dimukuradiyya irin Jamus, za ta yi kuskuran bai wa jam'iyyar kwaminisanci ta kasar Chaina damar yi mata aikin kafa hanyar sadarwar intanet mai karfi ta 5G. Domin a cewarsa kamfanin Huawei da Jam'iyyar kwaminisanci mai mulki a Chaina, tamkar kwaryar kasa ce da ta sama.

 Amirka da ma kwararru a fannin harakokin sadarwar yanar gizo a Jamus na fargabar ganin shigar kamfanin Huawei a aikin inganta harakokin sadarwar wayar salula a Jamus ya zamo wata kafa ga kasar ta Chaina ta gudanar da leken asiri ga Jamus da ma sauran kasashen Turai da Amirka.