Kashedi ga Najeriya kan batun tsaro | Labarai | DW | 23.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kashedi ga Najeriya kan batun tsaro

Kungiyar International Crisis Group mai nazarin rikice-rikice ta kasa da kasa, ta yi hannun-ka-mai-sanda ga Najeriya dangane da abun da ka iya kawo tadda zaune tsaye a lokacin zabe.

Zabubukan shekara mai zuwa ta 2015 na ci gaba da karatowa a Tarayyar Najeriya, yayin da ake ci gaba da samu tada jijiyoyin wuya tsakanin 'yan siyasa da ma tabarbarewar batun tsaro a wannan kasa.

Kashedin na International Crisis Group da ya fito a cikin wani rahoton da ta fitar mai shafi 42, na zuwa ne bayan wani hargitsi da aka fuskanta a majalisar wakilan kasar, bayan da jami'an tsaro na 'yan sanda suka yi amfani da borkonon tsofuwa a daidai lokacin isowar kakakin majalisar wakilan kasar, inda ake ganin iri-irin wannan yanayi ba zai haifar da da mai ido ba, inda wannan kungiya ta kara da cewa muddin dai ana so a kauce wa zubar da jini, to ala tilas sai an gaggauta samar da cikakken tsarin zabe da ma samar da cikakken tsaro ga zaben.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu