Kasashen Turai za su yi taro kan matsalar bakin haure | Siyasa | DW | 22.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kasashen Turai za su yi taro kan matsalar bakin haure

Taron kasashen Afirka da Turai ya mayar da hankali kan matsalar bakin haure masu neman shiga Turai inda ake samun masu mutuwa a cikin teku

Ana ci gaba da neman ganin kasashe masu karfi musamman na Turai sun dauki mataki kawo karshen bakin haure daga Afirka da Gabas ta Tsakiya, masu neman shiga Turai da ke mutuwa a cikin teku. A wannan Alhamis ake gudanar da taron musamman na kungiyar Tarayyar Turai kan matsalar.

Kasashen Afirka da na Turai na tunanin hanyoyin magance matsalolin da ke janyo bakin haure na kasadar neman tsallakawa domin shiga Turai ta tekun Baharrun inda mutane da dama ke mutuwa.

Taron gaggawa na shugabannin kasashen Turai zai duba hanyar magance matsalar. Wannan dai dai lokacin da gwamnatin kasar Italiya take ci gaba da aikin ceton rai a kan tekun.

Firaminista Matteo Renzi na kasar Italiya ya ce babban abun dubawa shi ne dalilan da suke janyo bakin haure ke yin tafiyar mai cike da hadari.

Renzi ya kara da cewa babban abin da ake bukata samar da cikekken mafita da hanyoyin ceton rayuka.

Kasar ta Italiya ta sake samun nasarar ceto wasu bakin haure fiye da 500 a kan tekun na Baharrun galibi 'yan kasar Siriya. Barbara Molinario ta hukumar kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ta nunar da halin da bakin hauren ke ciki wadanda ake kula da su.

Ana sa ran daukan matakin bai daya yayin taron gaggawa da kungiyar kasashen Turai za ta gudanar gobe Alhamis a birnin Brussels na kasar Belgium, domin samar da mafita kan dakile bakin hauren masu neman shiga Turai.

Firaminista Matteo Renzi na Italiya ya kira abin da ke faruwa da cinikin bayi na zamani ganin yadda masu fataucin mutane ke amfana da halin da bakin hauren suke ciki.

Kawo yanzu yawan bakin hauren da suka hallaka sun kai 2000 kuma idan aka kwatanta da yawan wadanda suka hallaka kimanin wannan lokaci a shekarar da ta gabata ta 2014 sun nunka sau 30, kamar yadda kungiyar kula da kauran mutane ta duniya ta nunar. Kungiyar ta ce akwai yuwuwar mutane 30,000 su halaka cikin wannan shekara bisa yunkurin shiga kasashen Turai ta Tekun Baharrun.

Galibin mutanen da ke mutuwa sun fito ne daga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kudu da Sahara na Afirka. Kifewar da jirgin ruwa ya yi dauke da bakin haure fiye da 800 wadanda suka hallaka a karshen mako ya zama hadari mafi muni da aka fuskanta kan tekun Bahurrun na masu neman shigowa kasashen Turai.

Sauti da bidiyo akan labarin