Kasashen Turai za su dauki mataki kan shige da fice | Labarai | DW | 20.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Turai za su dauki mataki kan shige da fice

Kasashen Turai na shirin kara matakin bincike kan iyakoki domin kare hare-haren 'yan ta'adda.

Ministocin cikin gida da na sharia daga kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun yi alkawarin ba da goyon baya ga Faransa bayan hare-haren birnin Paris da kusan mutane 130 suka hallaka. Ministocin sun yi alkawarin kara azama kan bincike a iyakokin kasashen da sauran kasashen da suke makwabtaka da kasashe 26 masu aiki da tsarin shige da fice iri daya.

Ministoci sun bayyana haka a birnin Brussels na kasar Blegium da ke zama helkwatar kungiyar.