Kasashen Turai na kai agaji Ukraine | Labarai | DW | 06.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Turai na kai agaji Ukraine

Har yanzu ana ci gaba da rikici tsakanin mahukuntan Kiev da kuma 'yan awaren gabashin kasar masu goyon bayan Rasha, duk kuwa da yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma.

Kasashen Turai sun tura jirage marasa matuka zuwa Ukraine, a wani mataki da suka ce na tabbatar da dorewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin mahukunta Kiev da kuma 'yan awaren gabashi da ke goyon bayan Rasha.

Haka nan ma wani babban jami'in Amirka ya kai ziyara Kiev din yayin da a hannu guda kuma Jamus ta aike da kayan agaji saboda hunturu ga yankunan da fada tsakanin dakarun gwamnatin Kiev da na 'yan aware ya dai-daita. Kawo yanzu dai mutane 3,300 ne aka hakikance sun mutu tun bayan da bangarorin biyu suka fara gwabza fada a tsakaninsu, a kokarin da 'yan aware masu goyon bayan Rasha ke yi na ballewa daga Ukraine.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo