1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsananin zafin Turai ya shiga kwana na 6

Ramatu Garba Baba
June 29, 2019

Akasarin kasashen Turai na ci gaba da fama da tsananin zafin da ya wuce kima wanda kuma hukumomi a kasashen suka ce an jima ba a ga irinsa ba.

https://p.dw.com/p/3LLOG
Spanien: Rekordhitze in Südeuropa
Hoto: Getty Images/AFP/J. Jordan

Kudancin kasar Faransa a wannan Asabar, zafin ya kai DigIri kimanin 46 a ma'aunin zafi na Celsius, inda ya haddasa gobarar da ta janyo asarar rayuka a wasu wurare. Baya ga Faransa wasu kasashe kamar su Italiya Spain na fama da tsananin zafi a wannan rana.

Ma'aikatar binciken sararin samaniyar Faransa ta ce matsalar na daukar dumi a arewacin kasar inda tsananin zafin da ke kadowa daga yankin sahara ke kara dagula al'amura wanda har ta kai ga yankin samun zafin da ya kai Digiri 38 a wannan Asabar. Yanzu haka dai kasashen Jamus Jamhuriyar Chek da Italiya ko wannensu na fuskantar Digiri akalla 38 zuwa 39.