Kasashen nahiyar Afirka na fama da bashi | BATUTUWA | DW | 12.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Kasashen nahiyar Afirka na fama da bashi

Kasashe da dama na nahiyar Afirka sun fara shiga cikin halin matsin tattalin arziki sakamakon annobar cutar coronavirus da ta shafi duniya baki daya.

Symbolbild | Dollar Scheine

Miliyoyin dalolin Amirka ake bin kasashen nahiyar Afirka bashi

Yayin da bashin da ake bin kasashen nahiyar ke kara habaka, a daya bangaren kudin shiga na kasashen na kara raguwa saboda annobar corona, lamarin da ka iya jefa harkokin rayuwa cikin karin matsaloli a fannoni masu muhimmanci na nahiyar. Kasashe kamar Angola, girman bashin da ake binta ya kai kaso 120 cikin 100 na kudin da kasar ke samu. Kuma a cewar ministan kudin kasar Vera Daves babu abin da suka saka a gaba illa ganin yadda rayuwa za ta ci gaba da tafiya. Kasashen da ke byar da bashi, sun yi alkawarin yafe wa kasar kimanin Euro milyan 1,300, a 'yan shekaru masu zuwa.

Karin Bayani: Tasirin Chaina a Afirka

A cewar Asusun ba da Lamuni na Duniya, ana bin kasashen Afirka kimanin Euro milyan dubu 410 da ake sa ran biya zuwa shekara ta 2023. Jürgen Kaiser da ke wata cibiyar kula da ci-gaban kasashe, na ganin lamarin na iya hargitsa kasashen: "Haka ya nuna kasashen ba sa iya katabus. Za a iya samun irin abubuwan da suka faru a kasashen arewacin Afirka, kamar yadda aka gani a yankin Sahel. Akwai Somaliya da ta dade. Gwamnati ba ta iya yin ayyukan da suka rataya a wuyanta musamman a fannin tsaro da ilimi da kuma kiwon lafiya. Wannan ya nuna mutane za su ga ba su da makoma a kasashensu."

Jürgen Kaiser

Jürgen Kaiser jami'i a wata cibiya da ke kula da ci-gaban kasashe

Tuni aka fara ganin karyewar tattalin arziki sakamakon annobar coronavirus da katse harkokin jin dadin marasa galihu a kasashe kamar Mozambik. Kuma rage yawan kudin bashin kadai, zai iya taimakawa kamar yadda Adriano Nuvunga na wata kungiyar fararen hula ke cewa: "Wannan yafewa na da tasiri ga Mozambik, saboda kasar tana bukatar kudi. Idan har sai Mozambik ta nemi kudin da za ta biya, yanayin zai zama mai sarkakiya. Fannin jin dadin mutane zai tabu, haka hanyoyin da za a nema domin taimakon marasa galihu, da iyalan da suke da tsananin bukata. Tun lokacin da annobar Covid-19 ta shafi kasar ba su samu tallafi ba, ba wani taimako."

Karin Bayani: Turai da Afirka na kokarin bunkasa arziki

Kasashen da suka dogara da man fetur kamar Gabon, gwamnati ta nuna kalilan na bunkasar tattalin arziki za a gani, Jürgen Kaiser da ke wata cibiyar kula da ci-gaban kasashe ya ce haka lamarin yake ga sauran kasashen. Tuni Bankin Duniya ya yi alkawarin taimakon wasu kasashe, kamar yadda suma kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya suka yi. Davin Malpass shugaban Bankin Dubniyar ya yi karin haske: "Wannan daga kafa a kan biyan bashi zai taimaka sosai, amma a tuna abin da haka zai yi, wato jan kafa wajen biyan bashi ga wasu kalilan na kasashe, suna bukatar rage yawan bashin da ake bin su. Sannan da kudin ruwa kalilan, kamar yanzu haka. Idan na ce ina bin ka miliyan dubu na dalar Amirka ka biya yanzu ko shekara mai zuwa, babu taimakon da aka maka sosai, saboda yana da matukar wuya ka fito da kudin."

Kasashen Yamma da Chaina ne a kan gaba wajen ba da bashi ga kasashen na Afirka.

Sauti da bidiyo akan labarin