Kasashen Larabawa za su dakile aiyyukan IS | Labarai | DW | 07.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Larabawa za su dakile aiyyukan IS

Ministocin harkokin waje na kungiyar kasashen Larabawa sun amince za su dauki matakan da suka kamata don dakile aiyyukan kungiyar nan ta IS da ke rajin kafa daular musulunci.

A wani zama da suka yi a kasar Masar, ministocin har wa yau sun ce za su yi aiki kafada da kafada da kasashen duniya da kuma dukannin kasashen da ke cikin kungiyar da nufin kawo karshen tada kayar baya ta 'yan kungiyoyin jihadi a yankin baki daya.

Taron ministocin ya kuma amince da kunshin wani kuduri da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi a watan jiya wanda ya nemi a katse dukannin wasu kafofi na samun makamai da tallafin kudi da masu kaifin kishin addini ke samu a kasashen Siriya da Iraki.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal