1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Chile ya kawo ziyar aiki Jamus

Zulaiha Abubakar
October 10, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sanar da shirin kara bunkasa alakar cinikayya a bangaren makamashi tsakanin Jamus da kasar Chile yayin da shugaban kasar Chile Sebastian Pinera ya ziyarceta a wannan Larabar.

https://p.dw.com/p/36JqS
Deutschland Besuch des chilenischen Präsidenten Pinera in Berlin
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Ta kuma kara da cewar kasancewar Chile kasar da ke da albarkar tagulla da sanholama ya zamar wa Jamus wajibi ta goyi bayan yarjejeniyar kasuwancin da kungiyar tarayyar Turai take dab da farfadowa da  kasar ta Chile, a nasa bangaren shugaba Pinera na Chile ya bayyana bukatar kasashen biyu su tattara bayanai tare da adana kayan tarihin yankin Colonia Dignidad in da wasu Jamusawa suka yi sansani yayin da suka yi hijira tun a shekara ta 1950.