Kasashen duniya sun yi tir da harin New Zealand | Siyasa | DW | 15.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kasashen duniya sun yi tir da harin New Zealand

Al'ummar Musulmi a wasu kasashen duniya sun yi zanga-zangar yin Allah wadai da harin da dan kasar Australiya ya kai a kasar New Zealand. Sai dai an tsaurara matakan tsaro don kare Musulmi a masallatan kasashen yamma.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na daga cikin shugabannin manyan kasashen duniya da suka fara mayar da martani tare da yin tir da harin ta'addancin da dan bindiga dan asalin kasar Australiya mai shekaru 28 ya kai kan wasu masallatai biyu lokacin sallar Jumm'a a birnin Christchurch na kasar New Zealand. Shi ma a nasa bangaren sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo, ta'aziyyarsa ya mika ga al'umar kasar New Zealand yana mai yin addu'a a madadin Amirkawa ga wadanda harin ya rutsa da su.


Firaministan Ostireliya Scott Morrison ya tabbatar da kasancewar maharin ne da zama dan kasarsa, kafin ya yi tir da danyen aikin da ya aikata a garin Christchurch da ke kudancin kasar New Zealand. Kafofin yada labaran kasar New Zealand sun ce hare-hare biyu aka kaddamar kan masallatan a wuraren ibadu dabam-daban. Mutane 49 ne hukmomin suka tabbatar da mutuwarsu a masallacin al Nuri da ke birnin na Christchurch

Sai dai bayanai sun tabbatar da cewar ya fito ne daga yankin New South Wales da birnin Sydney ke cikinsa. Ita ma Firaministar New Zealand din Jacinda Ardern ta yi tir da harin, yayin wani jawabin da ta yi. Ta ce: "A zahiri muna iya bayyana shi a matsayin harin ta’addanci. Daga abin da muka sani, hari ne da aka tsara shi da kyau. An sami wasu nakiyoyi biyu da aka makala a motocin wadanda ake zargi da hannu a lamarin da kuma aka kwance su. A halin yanzu ana rike da mutum hudu, kuma daya daga cikinsu ya tabbatar da cewa 'yan Ostireliya ne su. Wadannan mutane ne da ke da muguwar akida da sam-sam ba ta da gurbi a New Zealand, hasali ma a ko’ina a duniya."

UN-Generalversammlung in New York | Jacinda Ardern, Premierministerin Neuseeland

Fitaministar New Zealand Jacinda Ardern ta nuna kaduwa kan harin da aka kai kan masallaci.

  

‘Yan sanda sun ce babu alamun wata barazana kan wani masallaci a New Zealand bayan faruwar lamarin, kamar yanda shugaban 'yan sandan yankin Mike Bush ya tabbatar. Harin dai ya tayar da hankalin iyalai da dama, kasancewar masallacin na dauke ne da maza gami da mata da yawa.

 Mahmood Yassir da ya tsallake rijiya da baya ya ce: "Mutane sun damu da halin da iyalansu ke ciki. Ba a yi mana bayani da hankalinmu zai kama ba. Asibitoci ba sa cewa komai. Ko da jami’an ‘yan sanda ma ba su ce mana komai ba. Na tambayi wata daga cikin jami’an, wadda ke ce mani duk wani bayani kan iyalanmu zai iya kaiwa gobe. Don haka abin na da tashin hankali."

Shugabannin wasu kasashen Turai sun yi Allah wadai da hare-haren da aka kai wa Musulmin na New Zealand, kasar da ake ganin ba ta da masu aikata miyagun laifuka da suka kai wannan matsayi. 

Sauti da bidiyo akan labarin