Kasashen duniya sun yi Allah wadai da kissan masu bore a Masar | Siyasa | DW | 14.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kasashen duniya sun yi Allah wadai da kissan masu bore a Masar

Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai, da kuma kasashen duniya daban daban na yin suka ga matakan da dakarun tsaron Masar ke dauka a kan magoya bayan Mursi.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, ya bayyana takaicinsa dangane da zabin da hukumomin Masar suka dauka na yin amfani da karfin tuwo wajen fatattakar magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammed Mursi,da suka ce za su ci gaba da yi bore, har sai hukumomin sun mayar da shi a kan mulki. A cikin wata sanarwar da ofishin sakatare janar din, ya fitar, ya bukaci sassan da ba sa ga maciji da juna da su rungumi hanyar tattaunawa domin kawo karshen rikicin, game da mayar da kasar a bisa turbar dimokradiyya cikin lumana.

Ita ma Kungiyar Tarayyar Turai, ta bakin kantomar kula da manufofin ketare a kungiyar, Catherin Ashton, Allah wadai ne ta yi da tashin hankalin, tare da yin kira ga hukumomin Masar su nuna halin ya kamata wajen warware rikicin siyasar kasar, inda ta ce yin fto na fito, ba zai haifar da samako mai kyau ba.

Jamus ta yi Allah wadai da gwamnatin wucin gadin Masar

Shi kuwa ministan kula da harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, cewa yayi, gwamnatin Jamus na matukar nuna damuwarta dangane da hatsarin da ke tattare da ruruta wutar rikicin kasar, da jami'an tsaro ke yi:

Ya ce " Muna yin kira ga daukacin masu takaddama cikin harkokin siyasar Masar, da su koma kan teburin sulhu, domin hana rikicin ta'azzara. Tilas ne a dauki matakin kawo karshen ci gaba da zubar da jini a Masar."

A can kasar Turkiya kuwa, daruruwan masu zanga-zanga ne suka yi jerin gwano a kan titunan domin nuna rashin jin dadinsu dangane da tsauraran matakan da jami'an tsaron Masar suka dauka, da nufin dakile masu boren neman dawo da Mursi a bisa gadon mulki, inda ofishin fira ministan kasar Recep Tayip Erdogan, da ya sha yin kakkausar suka ga matakin kifar da gwamnatin dimokradiyya a Masar, ya ce, matakan da hukumomin suka dauka a yanzu, yana da hatsarin gaske ga kokarin sake dawo da kasar a bisa turbar dimokradiyya. Ya kuma yi Allah wadai da wasu kasashen da bai ambata sunansuba, wadanda ya zarga da nuna goyon bayan gwamnatin Masar, bayan hambarar da Mursi.

epa03824578 (FILE) A file picture dated 07 September 2010 shows Egyptian Interim Vice President Mohamed ElBaradei addressing a news conference in Cairo, Egypt. According to local media reports on 14 August 2013, ElBaradei has anounced his resignation from his post, hours after Egyptian security forces started clearing sit-ins of supporters of ousted president Morsi. Egypt's Health Ministry says that 149 people have been killed and more than 1,400 wounded in clashes across the country. EPA/MOHAMED OMAR *** Local Caption *** 50911526

El Baradei, mataimakin shugaban masar da yayi murabus

Tattaunawa ce mafita ga rikicin siyasar Masar

Ko da shike, Amirka ba ta fito fili ta ayyana kifar da gwamnatin Masar a matsayin juyin mulki ba, amma kakakin fadar shugaban Amirka, Josh Earnest, yayi Allah wadai da rikicin baya bayannan, wanda ya ce zai kawo cikas wajen sake aza kasar a bisa tafarkin ci gaba.

Dama, tun a makon jiya ne wasu 'yan majalisar dokokin Amirka da suka hada da Senata John McCain, suka yi kokarin shiga tsakani, inda McCain din ya mika bukata ga bangarorin biyu:

Ya ce Muna kira ga gwamnati da ta saki daukacin fursunonin siyasa, da kuma shirya zaman sasanta tsakanin al'ummar kasar Masar, da zai hada da kungiyar 'yan uwa Musulmi. Muna kuma fatan kungiyar za ta kaucewa tada rigima."

Kasar Iran, kamar dai ita kanta kungiyar 'yan uwa Musulmi ta hambararren shugaba Mursin, kwatanta matakin da jami'an tsaron Masar suka dauka ne ta yi da cewar, kissan kiyashi ne, game da yin kashedi a kan irin sakamakon da zai haifar, yayin da reshen kungiyar 'yan uwa Musulmi da ke kasar Jordan kuwa, ke karfafawa 'yan uwansu a Masar, gwiwar ci gaba da bore, har sai sun kai ga nasara, wadda suka ce ka iya taimaka wa fafutukar da kungiyar ke yi na dare madafun iko a sauran kasashen Larabawa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin