Kasashen duniya sun lale da kudurin MDD akan Lebanon | Labarai | DW | 12.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen duniya sun lale da kudurin MDD akan Lebanon

Sauran kasashen duniya ma sun yi maraba da kudurin wanda yayi kira ga Israíla da kungiyar Hisbollah a Lebanon da su tsagaita wuta nan take. Kudurin wanda kwamitin sulhu gaba daya ya amince da shi ya kuma tanadi kara yawan dakarun MDD a Lebabon ya zuwa dubu 15, sannan ya bukaci Isra´ila ta janye daga kudancin Lebanon. SGJ Angela Merkel ta bayyana kudurin da cewa wata kyakkyawar alama ce daga gamaiyar kasa da kasa. Shi kuwa babban sakataren MDD Kofi Annan ko da yake ya nuna rashin jin dadin sa ga jinkirin da aka samu kafin zartas da kudurin amma ya ce zai nemi sassan dake fada da juna da su amince da lokacin da zasu dakatar da yakin. Annan ya ce

„Bai dace ba in ki nuna muku rashin jin dadi na kan yadda kwamitin sulhun bai amince da kudurin tun tuni ba. Amma duk da haka zan tabbatar da cewa Isra´ila da Hisbollah sun amince da lokacin da shirin tsagaita wutar zai fara aiki.”