1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya sun kuduri aniyar kara kudin yaki da cutar AIDS

June 3, 2006
https://p.dw.com/p/BuvY

An kammala taron MDD akan cutar AIDS ko SIDA ba tare da daukar wani takamaimen alkawarin ba da karin kudin yaki da yaduwar cutar mai karya garkuwar jikin dan Adam ba. Bayan an shafe kwanaki 3 ana gudanar da taron a birnin New York, sanarwar bayan taron cewa ta yi kafin shekara ta 2010 za´a bukaci kudi kwatankwaci Euro miliyan dubu 18 a yaki da cutar ta AIDS a kowace shekara. Wannan adadin kuwa ya ninka har sau 3 yawan kudaden da aka kashe a bara don dakile yaduwar cutar. Duk da haka dai kasashe 151 da suka halarci gun taron sun sha alwashin kara yawan kudin da suke kashewa a yaki da cutar, to amma ba su kayyade lokacin ba da wadannan kudade ba.