1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya sun amince da rage yawan ma'adinin Uranium din da aka inganta

March 25, 2014

Taron da aka yi kan sha'ani na makamashin nukiliya ya amince da jerin abubuwa ciki har da dakile fadawar Uranium din da aka inganta a hannun 'yan ta'adda don gudun samun makamai na nukiliya.

https://p.dw.com/p/1BVgQ
Atomgipfel Den Haag Gruppenfoto 25.03.2014
Hoto: Reuters

A cikin sanarwa ta bayan taron na kwanaki biyu da aka kammala a wannan Talatar wanda shi ne karo na uku da aka gudanar da irinsa cikin shekaru 14 da suka gaba, bakin kasashen da suka hallarci taron dai ya zo daya inda suka bukaci da a tashi tsaye wajen ganin an dakile dukannin wani yunkuri na hana 'yan ta'adda kaiwa ga mallakar makaman kare dangi daga irin ma'adanin Uranium din da wasu kasashen duniya ke ingantawa.

Kazalika sanarwar bayan taron taron ta ce lokaci ya yi da kasashen duniya za su gama kai wajen inganta dokar da ta danganci tsaro na makamashin nukiliya baya ga batu na sanya idanu kan dukannin wani abu da ya danganci ingata ma'adanin Uraniun domin samun makamashi. Wannan ne ma ya sanya shugabanin da suka hallarci taron amincewa da fara shirin rage yawan irin ma'adanin Uranium din da aka rigaya aka inganta.

Niederlande G7-Treffen Krisengipfel in Den Haag Angela Merkel
Angela Merkel na kan gaba wajen neman rage yawan ma'adanin Uranium da aka ingantaHoto: picture-alliance/dpa

To sai dai duk da irin hadin kan da kasashen suka samu, 35 daga cikin kasashen 53 da suka hallarci taron ne suka yarda da girka wata doka ta kasa da kasa kan wannan batu yayin da kasashe 20 ba su sa hannu ba. Daga cikin wanda kasashe kuwa har da China da Rasha da Indiya da kuma Pakistan, lamarin ya sanya kwararru ke hangen irin jan aikin da ke akwai wajen cimma wannan nasara da aka sanya a gaba.

Irin rashin jituwa da ake samu a fagen siyasar kasashen duniya musamman ma dai abinda ke wanzuwa yanzu haka tsakanin Rasha da Ukraine wani abu ne da taron ya maida hankali a kai, wanda ya sa shugaban Amirka Barack Obama ya ce muddin Rasha ba ta kai ga sauya matsayinta ba to ta shirya marabtar karin takunkumi daga kasashen duniya.

Niederlande G7-Treffen Krisengipfel in Den Haag Barack Obama
Shugaba Obama ya ce za a sawa Rasha karin takunkumi in ba ta sauya rawa ba kan UkraineHoto: Reuters

Ya ce ''mun damu dangane da karin mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine, abinda na fada da wanda kungiyar EU ta ambata shi ne muna cigaba da yin shawarwari tare da tabbatar da cewar mun sanya komai inda ya dace dangane da kakabawa Rasha wasu jerin takunkumi muddin ta dauki wasu karin matakai nan gaba''

To sai dai duk wannan barazana ta Amirka da EU da ma sauran kasashen duniya gami da dakatarwa da da aka yi wa daga kungiyar G8 masu karfin arzikin masa'antu, Rashan ta ce ko a jikinta hasali ma in dai ana batu na Ukraine da Kirimiya ne da irin matsayin da ta dauka kan wannan dambarwa ta siyasa, bakin alkalami ya rigaya ya bushe. Wannan ne ma ya sanya ministan harkokin wajen Rashan Sergie Lavarov cewar fadar mulki ta Kremlin za ta fuskanci sauran batutuwa da ke gabanta ne.

Ya ce ''in dai wannan kungiyar ta taka irin wannan rawar kuma wasunsu sun yi na'am da ita, to mu kuwa kai tsaye za mu fuskanci wasu abubuwan musamman ma dai wanda suka danganci tattalin arziki da kudi a cikin kungiyar nan ta kasashen G20 da ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki a duniya.''

Russland Präsident Wladimir Putin
Rasha ta ce ba za ta sauya tunani ba kan matsayin da ta dauka a rikicin siyasa UkraineHoto: REUTERS

To yayin da wannan taro ya kammala, yanzu haka idanu na kasashen duniya da masu nazari kan lamura na yau da kullum sun karkata wajen ganin irin rawar da kungiyar G7 da ma ta sauran kasashen duniya da suka amince da matsayar da aka cimma a wannan taro za su taka wajen tabbatar da tsaro na abubuwan da suka danganci makamashi na nukiliya da fititunun da ke tattare da su gabannin makamancin irin wannan taro da za a gudanar a birnin Chicago na kasar Amirka cikin shekara ta 2016 idan Allah ya kaimu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar