1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Afirka sun mika bukata wa kotun duniya

October 12, 2013

Kungiyar Tarayyar Afirka ta nemi jinkirta hukunta shugabannin nahiyar da ke rike da mulki.

https://p.dw.com/p/19yYW
Hoto: picture alliance/ZUMAPRESS.com

Taron ministocin Kungiyar Tarayyar Afirka da a ka bude wannan Asabar (12. 10. 13) a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya amince da dakatar da kotun duniya daga hukunta shugabannin kasashen nahiyar lokacin da suke rike da madafun iko.

Ministocin harkokin waje daga kasashen 54, sun yi kirar jinkirta tuhumar da a ke yi wa Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto. Firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn ya nemi kotun ta duniya ta dubi wannan bukata da muhimmanci. Wannan jinkirtawa za ta shafi tuhumar da a ke wa Shugaban Sudan Omar Hassan al-Bashir, wanda kotun ta duniya ta ba da sammacin kamashi.

Sannan kungiyar ta Tarayyyar Afirka ta sanya hannu kan wani shiri na kara karfin rundunar kiyaye zaman lafiya da ke kasar Somaliya da kashi 35 cikin 100, domin yakar kungiyar 'yan tawayen Al-Shabab da ke da alaka da al-Qa'ida.

Kungiyar ta AU ta ce za ta kara dakaru fiye da 600, wanda hakan zai kara yawan dakarunta da ke Somaliya zuwa kusan dubu 24, in har kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da bukatar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh