1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana hanzarin arcewa daga Sudan

Abdul-raheem Hassan
April 24, 2023

Yayin da fada ke dada rincabewa a Khartoum babban birnin kasar Sudan, jiragen saman sojan Jamus uku na farko da suka fice daga Sudan sun isa kasar Jordan, wani jirgin iso da sauran mutane birnin Berlin.

https://p.dw.com/p/4QUaC
Sudan
Hoto: État-major des armées

Rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr ta yi nasarar kwashe mutane 313 daga Sudan cikin juragen sama guda uku zuwa kasar Jordan, tuni aka dawo da mutane sama da 100 zuwa Berlin.

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta kara da cewa, a yau Litinin, wani jirgin fasinja ya iso Berlin dauke da mutane 101. Kasashe da dama ciki har da Najeriya sun fara daukar irin wannan mataki na kwashe 'yan kasarsu daga cikin Sudan, a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada a babban birnin kasar, Khartoum, domin neman iko da Sudan.

Jiragen Faransa guda biyu sun kai kusan mutane 200 daga kasashe daban-daban zuwa Djibouti, Italiya ta kwaso mutane kusan 300 yayin da Ireland ta aike da tawagar gaggawa don taimakawa wajen tattara 'yan kasarta. Amirka ta kwashe mutane 100 cikin jirage masu saukar ungulu. Ita kuwa Birtaniya ta sallami wasu ma'aikatan diflomasiyya a cikin wani yanayi mai tsarkakiya.