1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus: Mutane na barin kasar China

Binta Aliyu Zurmi
January 29, 2020

Cutar Coronavirus na kara kamari a yanzu inda ta halaka mutum 134 a China a yayin da wasu sama da 5000 suka kamu da ita. Matsalar ta fi muni a yankin Wuhan inda ta samo asali.

https://p.dw.com/p/3WyWZ
Japan Coronavirus
Hoto: imago images/Kyodo News

Ministan lafiya na kasar Jamus, ya ce za su fara kwaso Jamusawan da ke China. Tuni kasashe kamar Amirka da Japan suka mayar da mutanensu gida. 

Bayanai sun ce Amirkawa kimanin 200 ne suka isa birnin California, bayan kwaso su da gwamnatin kasar ta yi.

Su ma kasashen Birtaniya da Faransa da Italiya dama wasu kasashen Turai su na gab da fara wannan shiri.