Kasar Turkiya ta ki neman afuwar Rasha | Labarai | DW | 30.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Turkiya ta ki neman afuwar Rasha

Firaministan Turkiya Ahmet Davatuglu ya bayyana wa kungiyar tsaro ta NATO a birnin Brussels cewar gwamnatinsa ba zata nemi afuwa bayan harbo jirgin Rasha ba.

Parteitag AKP Türkei Ahmet Davutoglu Plakat Flagge Ankara

Ahmet Davutoglu

Firaministan kasar Turkiya ya bayyana cewa kasarsa ba za ta nemi wata afuwa ba bayan kakkabo jirgin saman yakin Rasha da ke aikin fatattakar mayakan IS a Siriya bayan da ya ratsa samaniyar kasar ta Turkiya.

Firayim Minista Ahmet Davatuglu ya kuma bayyana cewa ya na cike da fatan ganin kasar ta Rasha ta sauya a kan matakin da ta dauka kan takunkumin tattalin arziki.

A ranar Litinin din nan kasar ta Rasha ta bayyana cewa za ta tsaida shigar da kayayyaki da suka shafi albarkatun gona musamman kayan gwari daga kasar ta Turkiya ko ma ta kara fadada takunkumin nan gaba idan bukatar hakan ta tashi.

Mista Davatuglu da yake jawabi a wani bangare na taron kungiyar tsaro ta NATO a birnin Brussels ya fada wa taron manema labarai a ranar Litinin din nan cewa shi ko shugaban kasar ta Turkiya ba wanda zai nemi afuwa a wurin kasar Rasha saboda abin da suka yi ya na bisa doron doka, sai dai a cewarsa kofar Turkiya a bude take ta tattauna da Rasha dan kaucewa sake afkuwar wannan matsala a nan gaba.