Kasar syria ta nanata matakin data dauka a game da | Labarai | DW | 10.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar syria ta nanata matakin data dauka a game da

Shugaban kasar Syria, wato Bashir Al Assad yace kasar sa ba zara mika kai bori ya hauba game da kokarin tursasa ta da ake neman yi game da abin da ya keta dokar kasa da kasa.

, Al assad wanda ya fadi hakan yayin da yake jawabi a Jami´ar Damascus a yau din nan yaci gaba da cewa, kasar sa ba zata taba canja matakin da data dauka a game da zarghin da ake mata ba game da rasuwar tsohon Faraministan kasar Labanon wato Rafik Hariri.

Bugu da kari Al Assad ya kara da cewa ire iren suka da kasar sa take fuskanta ba wani abi bane illa kafa da ake son samu don haifar da tsugune tashi a cikin kasar.

To Amma duk da wadan nan bayanai na Bashir Al Assad, Shugaban na Syria yace kasar sa zata ci gaba da bawa Jami´an Mdd goyon baya naci gaba da gudanar da binciken wadanda keda hannu a cikin dana bon din daya tashi da Tsohon Faraministan na Labanon tare da wasu sama da Dozin daya.