Kasar Ruwanda da Somaliya sun dauki hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 20.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Kasar Ruwanda da Somaliya sun dauki hankalin jaridun Jamus

Taron kasa da kasa kan kasar Somaliya da kuma gargadin kotun kasa da kasa ta ICC game da shari'ar shugabannin Kenya sune jaridun Jamus suka duba a wannan mako.

To madallah. Jaridun na Jamus sun tabo al'amura masu yawa a sharhunansu na wannan mako kan Afirka.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung alal misali, tayi magana kan zaben majalisar dokoki da aka yi a Ruwanda a wannan mako, inda tace tun ma kafin zaben, jam'iyar shugaban kasa Paul Kagame ita ce aka sa ran zata lashe wannan zabe saboda shi kansa shugaban har yanzu yana da matukar farin jini a kasarsa. Wannan hange kuwa shi ya tabbata, domin jam'iyar kishin kasa ta Rwanda karkashin Kagame ita ce ce ta lashe zaben tare da babban rinjaye, na abin da ya kai kashi 76 cikin dari. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace angizon Kagame a siyasar kasar ta Ruwanda ma zai fi haka karuwa, saboda wasu jam'iyun guda biyu da gaba daya suka sami kashi 22 cikin dai na kuri'un da aka kada, suna da dangantaka ta kurkusa da jam'iarsa. Jaridarar tace sai dai kuma ko da shike jam'iyu masu yawa sun shigar da yan takara a zaben na Ruwanda, amma ba za'a ce jam'iyu na adawa suna da wani karfi na tafiyar da aiyukan su kamar yadda tsarin mmulkin kasar ya tanadar ba.

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung tayi sharhi ne a game da gargadin da kotun kasa da kasa dake birnin The Hague, tayiwa duk wadanda suke da shirin tona asirin mutanen da aka gaiyata, domin su bada shaida a shari'ar da ake yiwa shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta da mataimakinsa, William Ruto. Kotun ta ICC tace akwai rahotannin dake nuna cewar tuni an fara tona asirin wasu daga cikin wadannan shaidu, inda ata ma tace tun da aka gabatar da sunanta a kaofin sadara ko cudanya na zamani, ta fara jin tsoron ranta. Kotun dake shari'ar shugabannin na Kenya guda biyu, saboda zarginsu da aka yi da laifkan kisan ar dangi, tattare da tashin hankalin da ya biyo zaben shugaban kasada na majalisar dokoki a Kenya a shekara ta 2007, ta kare shaidun nata ne ta hanyar basu lambobi, maimakon sunaynsu na asali. Jaridar Süddeutsche Zeitung ta ambaci kakakin hukumar kare hakkin yan Adam ta Kenya tana cewar burin wadada suka bankada sunan wannan mata shine su tsorata sauran shaidu, yadda wadanda ake tuhuma zasu fice daga kotun na birnin Hague ba tare da an yi masu hukunci kan laifukan da suka aikata ba.

Somalia Geberkonferenz in Brüssel 16.09.2013

Taron kasa da kasa a Bruessels kan Somaliya

A wannan mako, jaridar Frankfurter Allgemeine Zaitung ta kuma duba taron kasa da kasa da aka yi kan Somaliya a Bruessels ranar Litinin da ta wuce. Wannan taro, kamar irinsa aka saba yi jefi-jefi kan kasar ta Somaliya, an yi shi ne domin nemarwa kasar taimakon kudi . A wannan karo kasashe da kungiyoyin a suka halarci taron sun yi alkawarin tara abin da ya kai Euro miliyan dubu daya da 800. Daga cikin wannan adadi, Kungiyar Hadin Kan Turai ita kadai tace zata bada gudummuwar Euro miliyan 650 ga kasar ta yankin Kahon Afirka, yayin da Jamus tace zata bada taimakon Euro miliyan 90, bisa sharadin gwamnatin Somalia zata dauki matakan kyautata batun kar hakkin yan Adam da kuma ganin an sulhunta rikicin dake addabar wannan anki cikin lumana. A kasar ta Somaliya tun bara aka kafa gwamnatin da ta sami karbuwa ga yan kasar da kasashen ketare masu bata taimako. Batun tsaro a cikin kasar da tayi fiye da shekaru 20 tana fama da yakin basasa daga haulolin yankunanta dabam dabam ya kyautata, tun da Kungiyar Hade Kan Afirka ta AU ta tura sojojin rundunar AMISOM wadanda suka sanya kafar wando daya da kungiyoyin masu dauke da makamai.

Mawallafi: Umarau Aliyu
Edita: Mouhamadou Awal