1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Kuba za ta sami sabon shugaba

Zulaiha Abubakar
April 19, 2018

Gwamnatin kasar Cuba ta zabi Diaz-Canel mataimakin shugaban kasar a matsayin wanda zai maye gurbin shugaba Raul Castro don tabbatar da dorewar kasar bisa tsarin jam'iyya daya.

https://p.dw.com/p/2wInU
Kuba Raúl Castro und Miguel Díaz-Canel
Hoto: Getty Images/AFP/J. Beltran

Wannan sauyi na zuwa ne bayan da 'yan majalisar dokokin kasar suka amince da zaben sabon shugaban kasar wanda ba shi da dangantaka da iyalan Castro a karon farko bayan Iyalan Castro sun shafe tsawon lokaci suna mulkin kasar.

Raul Castro zai ci gaba da jagorantar jam'iyyar Kwamunisanci mai mulki a kasar duk kuwa da cewar ya amince ya mika mulkin kasar ga Diaz, sai dai ya shaidawa manema labarai cewar zai sauka ne daga mulkin don baiwa sabbin shugabanni damar tafiyar da al'amuran kasar, daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsin tattalin arziki tare da wariya daga sauran kasashen

Ya zuwa yanzu dai al'ummar kasar na fatan wannan sauyi zai ciyar da kasar Gaba.