1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Habasha ta haramta tallan barasa

Yusuf Bala Nayaya
April 9, 2019

Matakan hanawar sun hadar da hana duk wani tsari na ba da kyautar giya ga masu yin caca ko sanya manyan alluna a kan titi don tallata barasar.

https://p.dw.com/p/3GWg5
Schottland Alkohol Verkauf
Hoto: picture alliance/dpa/empics/PA Wire/J. Barlow

Ma'aikatar lafiya a kasar Habasha ta bayyana a wannan Talata cewa ba a yarda ba a ga ana tallata duk wani nau'i na abin sha mai dauke da barasa, matakin da ke zuwa cikin jerin tsare-tsare da kasar ke dauka wajen tabbatar da ganin mutane na rayuwa cikin koshin lafiya.

Matakan haramcin sun hadar da hana duk wani tsari na ba da kyautar barasa ga masu yin caca koma sanya manyan alluna a kan titi don tallata barasar kamar yadda ministan lafiya Amir Aman ya fada wa manema labarai.

Wannan hani dai na zuwa ne bayan tun da fari gwamnatin kasar ta hana shan taba sigari a kusa da gine-ginen gwamnati. A watan Fabrairun da ya gabata baya ga hani na shan sigarin kusa da ma'aikatun gwamnati, da ma'aikatu masu kula da harkokin lafiya da wuraren shakatawa an kuma haramta sayar da barasar ga mutanen da ke kasa da shekaru 21 da haihuwa.